Yadda Zaka Fara Samun Kuɗi a Fiverr da Upwork (Jagorar Mataki-da-Mataki)

Gabatarwa Idan kana son fara freelancing , shafuka biyu da suka fi sauƙi su ne Fiverr da Upwork . A wannan rubutu, zan nuna maka yadda zaka fara daga tushe – daga buɗe account, yin profile, ƙirƙirar gig , har zuwa samun client naka na farko. Mataki 1 – Buɗe Account Fiverr: Je zuwa www.fiverr.com ka yi Sign Up da email ko Google account. Upwork: Je zuwa www.upwork.com ka yi Sign Up . Tabbatar ka saka sunan da ya dace, domin profile ɗinka zai zama kamar CV naka online. Mataki 2 – Gina Profile Mai Kyau Abubuwan da suka fi muhimmanci a profile: Profile Picture: Professional (ba sai ka saka suit ba, amma kada ya zama hoton wasa). Title: Misali – “SEO Specialist | Content Writer | Social Media Manager” Description: Rubuta taƙaitaccen bayanin kanka, skill ɗinka, da irin abinda zaka iya yiwa client. Skills: Zaɓi keywords da suka dace (misali SEO, Article Writing, Email Marketing). Portfolio (samples): Ka saka samfurin ayyuka da kayi (ko test pro...